14 Agusta 2021 - 13:49
Madagaska : Shugaba Rajoelina, Ya Kori Dukkan Ministocinsa

Shugaba Andry Rajoelina, na Madagaska ya kori dukkan ministocinsa, saidai tare da jadada yarda ga firaministansa Christian Ntsay.

ABNA24 : A halin yanzu dai ministocin da aka kura zasu tafiyar da aikinsu ne kawai kafin a nada sabbi da zasu gaje su nan gaba.

Matakin dai na zuwa ne a daidai lokacin da kotun kasar ke binciken yunkurin juyin mulkin da bai yi nasara ba, wanda bayansa aka cafke kimanin mutane ashirin cikinsu har da faransawa biyu da wasu mayan jami’an kasar da dama.

A ranar 20 ga watan Yulin da ya gabata mutane shida har da faransawan biyu aka cafke a binciken da ake ci gaba da yi kan laifukan da suka hada da cin amanar kasa, da kuma shirin hallaka manyan jami’ai da dama na kasar ciki har da shugaban kasar Andry Rajoelina.

Masharhatan da dama dai na ganin da wuya a sake dawo da ministocin da ake ganin suna da hannu a yunkurin juyin mulkin a daidai lokacin da ake shirye shiryen manyan zabukan kasar na 2023.

342/